Na'urar bincike a cikin teku na kasar Sin Jiaolong ya yi nutsewar farko a teku mai zurfi na Yap Trench a jiya Lahadi.
Jiaolong ya fara nutsewa ne da misalin karfe 8 da minti 43 na safe agogon wajen, a lokacin da ake ruwan sama, inda ya kai nisan mitoci 4,177.
Na'urar za ta nutse a yankin tekun har sau biyar, inda za ta yi ta karshe a ranar 12 ga watan Yuni.
A cewar masana kimiyya dake cikin jirgin ruwan, nutsewar za ta mai da hankali ne kan binciken halittun cikin teku da albarkatu.
A ranar 1 ga watan Yuni ne na'urar Jiaolong ta kammala aikinta a sashen teku mafi zurfi na duniya wato Mariana Trench, inda kuma jirgin bincike na Xiangyanghong ya dauke ta zuwa Yap Trench.
Wannan ne karo na 3 kuma mataki na karshe na binciken kimiyya cikin teku, na kasar Sin karo na 38, wanda aka fara a ranar 6 ga watan Fabrairu, kuma aka sa ran kammalawa a ranar 18 ga watan Yuni.
Na'urar ta yi nasarar kammala matakai biyu na baya ne a cikin tekun Indiya da tekun kudancin Sin. (Fa'iza Mustapha)