Nutson na ranar Talata dai shi ne na 4 da jirgin ya gudanar a wannan shekara. Rahotanni sun bayyana cewa jirgin ya fara nutson ne da misalin karfe 7:03 na safe, ya kuma isa nisan da aka tsara da misalin karfe 10:21 na safe.
Masu binciken dake cikin jirgin na Jiaolong sun shafe sa'o'i 3 da mintuna 10 kafin kammala ayyukan da suka gudanar da su a karkashin ruwan. Sun kuma samu nasarar debo samfuran nau'o'in duwatsu, da marmara, da wasu halittun ruwa, da ma ruwan teku mai zurfi.
Daya daga masu binciken da ya halarci wannan aiki Peng Xiaotong, ya bayyana muhimmancin nazarin rayuwar kifayen musamman na karkashin teku, yana mai cewa hakan zai bada damar gano yanayin sauyin rayuwar su, da yadda muhalli ke tasiri ga sauyin da suke fuskanta.
Jirgin nutso na Jiaolong dai ya gudanar da aikin sa a yankin teku na Mariana a karon farko cikin wannan shekara ta bana a ranar 23 ga watan nan na Mayu, inda dan jarida Liu Shiping, ya kasance cikin tawagar masu nutson mai zurfin mita 4,811. Kaza lika ya sake yin nutson mita 6,300 a karo na biyu, a ranar 25 ga wata, yayin da kuma ya yi nutso na uku na mita 6,544 a ranar 27 ga wata.