in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban kwamandan Al-Shabaab ya mika wuya
2017-06-01 10:30:50 cri

A ranar Laraba wani babban kwamandan kungiyar Al-Shabaab Bishar Mumin Farah, ya mika wuya ga dakarun sojin kasar Somalia (SNA) dake zaune a yankin Hiiraan a tsakiyar Somalia.

Ministan yada labaran Somalia Abdirahman Omar Osman, ya tabbatar da cewa, 'dan tada kayar bayan shi ne kwamandan kungiyar dake yankin Mudug.

Osman ya ce, kwamandan Al-Shabaab na Mudug din, ya mika wuya ne ga dakarun sojin Somalia a yankin Hiiraan.

Kwamanda rundunar ta 52 na SNA janar Mohamed Ahmed, ya bayyana cewa, Farah yana dauke da bindigogi samfurin AK 47 guda biyu a lokacin da ya mika wuyan.

A cewar Osman, kwamanda na Al-Shabaab da ya mika wuya, ya kasance mai kula da yakin sari ka noke na kungiyar, kuma ya je yankin Hiiraan ne da nufin kaddamar da sabon yaki a lokacin azumin watan Ramadan, sai dai mika wuyan da ya yi babbar hasara ce ga kungiyar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China