in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Al-Shabaab ta dauki alhakin harin bam a jirgin saman Daallo
2016-02-14 10:40:56 cri

Kungiyar tada kayar baya ta Al-Shabaab ta dauki alhakin harin bam na jirgin saman Daallo a makon da ya gabata, kuma ta bayyana hakan a matsayin wani yunkuri na yaki da Turawan yammacin duniya da dakarun hadin gwiwa na NATO da kasar Turkiyya wadanda ke zaune a kasar Somaliya.

A sanarwar da kungiyar ta fitar a ranar Asabar din da ta gabata, ta bayyana harin a matsayin ramuwar gayya game da barnar da jami'an kawancen hadin gwiwa na Turawan yamma da hukumomin leken asiri ke aiwatarwa kan Musulmi a Somaliya.

Sanarwar ta zo ne a yayin da tawagar jami'an bincike da gwamnatin Somaliya da kuma ofishin bincike na musamman na Amurka suka fara kaddamar da bincike game da musabbabin hadarin jirgin saman ko yana da alaka da ta'addanci.

Shi dai jirgin saman na Daallo ya yi saukar gaggawa ne mintuna 35 da tashinsa daga filin jirgin saman Aden Adde na Mogadishu a makon jiya.

Ya zuwa yanzu, mutane sama da 40 ne aka damke bisa zarginsu da hannu a harin.

Kungiyar Al-Shabaab tana zargin Turkiyya da laifin zama guda cikin mambobin dakarun tsaron hadin gwiwa ta NATO, inda Turawan yamma ke amfani da ita wajen yaki da addinin Islama da mabiya Musuluncin a Somaliya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China