in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Somaliya sun damke wani jigon mayakan Al-Shabaab
2016-02-24 09:49:54 cri

Dakarun tsaron kasar Somaliya sun yi nasarar kama daya daga cikin jiga-jigan mayakan Al-Shabaab a wani otel dake Mogadishu,babban birnin kasar.

Hukumar tsaron farin kaya ta kasar (NISA) ta tabbatar da wannan kame cikin wata sanarwa da ta rabawa manema labarai a jiya Talata, sai dai ba ta bayyana sunan mutumin da ta kama a otel din da ke kasuwar Bakaro ba.

Hukumar ta ce, mutumin da ta kama tare da wasu mayakan kungiyar, yana daga cikin wadanda kungiyar da ke ji da su. Yanzu haka dakarun tsaron kasar ta Somaliya na ci gaba da yi musu tambayoyi.

Jami'an na NISA sun ce, nan ba da dadewa ba za su bayyana sunansa. Sai dai har yanzu kungiyar ta Al-Shabaab ba ta ce komai ba game da jami'in nata da aka kama.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China