in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shirya taron gabatar da shirye-shiryen hadin gwiwa tsakanin lardin Hebei na kasar Sin da jihar Kaduna ta Najeriya
2017-05-23 11:16:30 cri

A yayin taron, wani wakilin kamfanin samar da na'urorin aikin gona na lardin Hebei ya bayyana fatansa na yin hadin gwiwa da bangaren Najeriya, inda ya bayyana cewa, "Muna samar da na'urorin girbin masara da alkama da kuma wake. Suna daga cikin muhimman amfanin gona na jihar Kaduna. Ina son sani idan muna son yin hadin gwiwa da jihar Kaduna, wane irin mataki ne jihar Kaduna za ta dauka domin taimakawa wajen kera na'urorin aikin gona a jiharku?"

Game da tambayar, malam Kabiru Mato, kwamishinan ma'aikatar gona da gandun daji na jihar Kaduna ya ba da amsa cewa, "Dazu ka ambaci na'urorin aikin gona, ciki har da na'urorin girbin amfanin gona. Yanzu muna neman damar yin hadin gwiwa, kuma muna son sayen wasu na'urori masu alaka. Ina fatan ba wai za a iya sake tattaunawa kan batun a tsakaninku da gwamnatin jiharmu kawai ba ne, har ma a tsakaninku da manoma da kamfanoni na jiharmu, domin neman damar shigar da kayayyakinku a jiharmu."

An labarta cewa, a lokacin da tawagar wakilan tattalin arziki da cinikayya ta jihar Kaduna take lardin Hebei, ta yi rangadi a biranen Shijiazhuang, fadar mulkin lardin, da birnin Xingtai, inda ta kai ziyara a wasu kamfanonin kasar Sin, har ma ta daddale wasu yarjejeniyoyin yin hadin gwiwa na fahimtar juna da lardin Hebei da kamfanin CCECC. (Sanusi Chen)


1  2  3  
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China