in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shirya taron gabatar da shirye-shiryen hadin gwiwa tsakanin lardin Hebei na kasar Sin da jihar Kaduna ta Najeriya
2017-05-23 11:16:30 cri

Game da wannan sabon salon hadin gwiwa, Mr. Zhao Tianlong, babban direktan kamfanin CCECC ya bayyana cewa, "Ya kasance wani kamfanin mallakar gwamnatin tsakiya dake aiki a ketare, kamfanin CCECC yana son yin amfanin da albarkatun zaman al'umma da ya samu a tarayyar Najeriya ciki har da jihar Kaduna domin nuna goyon baya ga wannan salon hadin gwiwa. Sakamakon haka, lardin Hebei da jihar Kaduna da kamfaninmu CCECC za su iya samun ci gaba da moriya tare. Bugu da kari, kamfanin CCECC yana son zama mai yin jagora don kulla alaka tsakanin kamfanonin lardin Hebei da na jihar Kaduna a lokacin da suke kokarin yin hadin gwiwa."

Jihar Kaduna jiha ce mai arzikin ma'adinai. Har ma tana kan gaba wajen bunkasa masana'antu da aikin gona a Najeriya. Gwamna Nasir El-Rufa'i na jihar Kaduna ya fadawa wakilan sashen Hausa na CRI cewa, jiharsa tana son kara yin hadin gwiwa da kasar Sin a fannonin aikin gona da shirye-shiryen zirga-zirga. Mai girma Nasir El-Rufa'i ya ce, "Muna neman taimakon gwamnatin kasar China da lardin Hebei wurin bunkasa aikin noma a jihar Kaduna, da kuma daukan kayan noma a sarrafa su ta yadda za a iya fitar da su a sayar da su a kasashen waje. Muna kuma fatan gwamnatin kasar Sin za ta taimaka mana wurin kara layin dogo a cikin garin Kaduna, ba wai kawai tsakanin Kaduna da Abuja ba, a'a. muna fatan sa layin dogon a cikin garin Kaduna, muna son hade Kaduna da Zaria, misali muna son mu hada Kaduna da Kamfancha. Mu muna neman taimakon kasar Sin wajen yin wannan."

1  2  3  
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China