Taron ya samu halatar shugaban Amurka Donald Trump da kuma shugabannin kasashen Musulmi 55.
Yayin taron, an kuma kaddamar da wata cibiya a Riyadh, wadda ke da nufin sa ido da kuma kawar akidar kaifin ra'ayin addini.
Riyadh ta karbi bakuncin taruka uku a ranakun Asabar da Lahadi yayin ziyarar Donald Trump a kasar Saudiyya, wanda shi ne tafiyar da ya yi ta farko tun bayan darewarsa karagar mulki. (Fa'iza Mustapha)