Mai taimakawa shugaban kasar Sudan, kana mataimakin shugaban kwamitin raya hulda da kasar Sin, Awad Ahmed Jaz, ya bayyana cewa, Sudan na maida hankali sosai kan habaka dangantaka tare da kasar Sin, tana kuma fatan amfani da damar bunkasa 'ziri daya hanya daya', wajen kara karfafa hadin-gwiwa da mu'amala tare da Sin, a wani mataki na cimma moriya tare.
Jaz ya kara da cewa, kasarsa wato Sudan ta gabatarwa kasar Sin wasu sabbin shirye-shirye da za ta iya zuba jari a ciki, wadanda suke shafar fannonin man fetur, ma'adinai, zirga-zirgar jiragen sama, ayyukan gona, yawon shakatawa da sauransu, yana kuma fatan kamfanonin kasar Sin za su kara zuba jari a kasar ta Sudan.(Murtala Zhang)