Awad Ahmed Al-Jaz, wanda shi ne jami'i mai kula da tabbatar da dangantaka tsakanin Sin da Sudan ya fada a lokacin zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewar, wannan shawara mai muhimmanci ta kunshi wani jadawali wanda zai samar da cigaba a tsakanin dukkannin kasashen duniya.
Ya kara da cewa, shirin na ziri daya hanya daya ya kunshi muhimmin nauyi a bisa matsayin koli wanda shugabancin kasar Sin yake da muradin saukewa bisa gaskiya da kuma burin dukkan kasashen duniya su ci gajiyar shirin wajen samun ci gaba. Wannan shawara damkar wani jakaran gwajin dafi ne wanda ya tattaro tunani mai zurfi domin yin aiki tare don cimma nasarar ta hanyar shigar kowane bangare don a dama da shi.
Al-Jaz, ya kuma yabawa muhimmin jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a ranar Lahadi a lokacin kaddamar da bude taron hadin kai na kasa da kasa kan shawarar ziri daya hanya daya a birnin Beijing, kana ya yabawa kalaman da shugaba Xi ya gabatar, inda ya tabbatarwa duniya cewa, kasar Sin ba za ta yi shisshigi game da ikon kowace kasa ba a duniya. (Ahmad Fagam)