in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta sanar da sabon zagayen tattaunawar sulhu a Sudan
2015-11-11 10:38:47 cri

Kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU a ranar Talatan nan ta sanar da sake dawo da tattaunawar sulhu a ranar 18 ga wannan wata tsakanin gwamnatin kasar Sudan, kungiyar SPLM bangaren arewa, da kuma kungiyar Darfur masu dauke da makamai a birnin Adis Ababa, na kasar Habasha.

Kungiyar ta AU ta aika da sakon gayyata ga ministan harkokin wajen kasar Sudan Ibrahim Ghandour da shugabannin kungiyoyin masu dauke da makamai, in ji Mahmoud Kan, shugaban ofishin AU dake birnin Khartoum.

Da yake bayani ga manema labarai, Mahmoud Kan ya ce, tattaunawar sulhun za ta wakana ne tsakanin gwamnatin Sudan da kungiyar Darfur Movements, sannan kuma tsakanin gwamnatin Sudan da kungiyar SPLM bangaren arewa a ranakun 18 da 19 na wannan watan na Nuwamba. Ya yi bayanin cewa, a baya zagaye 9 na tattaunawar tsakanin gwamnatin kasar Sudan da kungiyar SPLM bangaren arewa ya gaza cimma mafita wajen kawo karshen rikici tsakanin bangarorin biyu. An yi tattaunawar ta karshe a watan Disambar shekarar bara.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China