in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana da kyakkyawar makoma kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Somaliya
2016-12-08 19:54:17 cri

Jakadan kasar Somaliya dake kasar Sin Yusuf Hassan Ibrahim ya bayyana a jiya Laraba cewa, akwai kyakkyawar makoma a hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Somaliya a dukkan fannoni, a don haka, yana maraba da kamfanonin Sin da su zuba jari a kasar Somaliya.

A jiyan ne kuma jakada Ibrahim ya ziyarci jami'ar koyon harsunan waje ta Beijing, inda ya bayyana cewa, Somaliya da Sin suna bukatar juna a fannonin da suke da kwarewa, kasar Somaliya tana da albarkatun halittu, wanda zai iya taimakawa ga ci gaban kasa, kana kasar Sin tana da karfin taimakawa kasar Somaliya wajen kara samun ci gaba.

Haka zalika kuma, jakada Ibrahim ya ce, Somaliya da Sin sun dade suna sada zumunta da juna, Sin ita ce kasa ta biyu mafi karfin ci gaban tattalin arziki a duniya. Ko da yake Somaliya tana fuskantar barazanar yakin basasa da ta'addanci, amma duk da haka ya yi imani cewa, za a ci gaba da raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, kuma Sin tana da karfin taimakawa kasar Somaliya ta yadda za ta samu ci gaba tare da samun moriyar juna. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China