Yanzu haka kamfanin yana son aiwatar da wasu tsare-tsare guda uku. Na farko, samar da makamashi mai tsafta, na biyu, wadataccen makamashi, kana na uku, raba makamashi dai-dai da bukatan masu amfani da shi. Kamar a gidaje, makarantu, masana'antu, unguwanni da sauransu.
ENN yana da rassa sama da 160 a fadin kasar Sin, yana kuma kokarin gina tashoshin samar da makamashi mai tsafta a sassan kasar. Bayanai daga jami'an kamfanin ya nuna cewa, wani muhimmin aikin da kamfanin ya himmatu a kai shi ne samar da makamashi ta hanyar amfani da iskar gas ba tare da gurbata muhalli ba, da kuma samar da makamashi daga tsirrai.
Tun daga shekarar 2014 ne dai kasar Sin ta mayar da hankali wajen bullo da hanyoyin amfani da makamashi mai tsafta, a wani mataki na rage gurbata muhalli.(Ibrahim Yaya)