in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
(Ziyarar da wakilinmu Ibrahim Yaya a lardin Hebei) Na kai ziyara kamfanin harhada magunguna na Yiling dake Shinjiazhuang
2017-05-09 10:44:22 cri

 

 

Kamfanin harhada magunguna na Yiling yana daya daga cikin kamfanonin da suka shahara wajen harhada magungunan gargajiya da na zamani da gudanar da bincike a harkar inganta lafiyar bil-Adam a kasar Sin.

Kamfanin Yiling wanda aka kafa shi a shekarar 1992, yana samar da magungunan da suka hada da na ciwon zuciya da ciwon koda da maganin narkar da abinci,da jijiyoyin kwakwalwa. Sauran sun hada da maganin da zai taimaka wajen yakar murar tsuntsaye nau'in H9N2, SARS, da EV71 da maganin Mura har ma da tari.

Baya ga magungunan gargajiya da na zamani, kamfamin Yiling, ya tanadi wata cibiyar lafiya, inda ake sayar da na'u'o'in abinci da kamfanin yake samarwa da wadanda yake shigo dasu daga abokan hulda,kamar biskit, da kwan kaji, da shayin rage kiba da gyara jiki da sauransu.

Kamfanin Yiling dake garin Shijiazhuang a lardin Hebei, yana da rassa a kasashen Amurka da Burtaniya, kana ya zuwa yanzu kamfanin yana fitar da kayayyakinsa zuwa kasashen koriya ta kudu,da Ingila da, Canada, da Netherlands, da Singapore da Rasha da sauransu.

Jami'an kamfanin Yiling sun shaidawa manema labarai cewa, kamfanin yana da ma'aikata sama da dubu 5 baya da kwararrun masu gudanar da bincike kan cututtuka da harhada magunguna masu tarin yawa, kuma yana gudanar da ayyukansu ba tare da gurbata muhalli ba.

Bayanai na nuna cewa, kamfanin Yiling yana taka muhimmiyar rawa wajen samar da guraben aikin yi da kudaden shiga a lardin Hebei har da kasar Sin baki daya, baya da muhimmiyar rawar da kamfanin yake takawa a fannin kiwon lafiyar jama'a.(Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China