in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
(Ziyarar wakilinmu Ibrahim Yaya a lardin Hebei) Na kai ziyara kamfanin samar da na'urorin wutar lantarki na Kelin dake birnin Shijiazhuang
2017-05-10 08:44:57 cri

An kafa kamfanin samar da na'urorin wutar lantarki mai zaman kansa na Kelin dake garin Shijiazhuang ne a shekarar 2000, kuma yanzu haka kamfanin yana daga cikin fitattun kamfanonin samar da na'urorin wutar lantarki a kasar Sin.

Kayayyakin da kamfanin ke samarwa sun hada da na'urorin daidaita wutar lantarki da na'urar samar da makamashin da ake iya sabuntawa da farentan samar da wutar lantarki bisa karfin hasken rana. Sauran sun hada da mitocin wutar lantarki da ake makalawa a gidaje, kuma yanzu haka ana amfani da irin wadannan kananan mitocin wutar lantarki a kasashen Angola da Najeriya, da kanana da manyan na'urorin cajin motoci masu amfani da wutar lantarki.

Kamfanin yana da ma'aikata sama da 1,000 da kuma masu bincike kimanin 200, yana kuma amfani da kashi 5 cikin 100 na ribar da ya inganci wadanda ba su da illa ga muhalli.

1  2  3  4  
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China