in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta bunkasa shirin PPP a bangarorin aikin gona da yawon shatakawa
2017-05-04 10:03:50 cri

Gwamnatin kasar Sin ta bayyana kudurinta na bunkasa shirin hadin gwiwa tsakanin gwamnati da sassa masu zaman kansu, a wani mataki na bunkasa bangarorin aikin gona, yawon shatakawa, da al'adu da kuma sashen kiwon lafiya.

Wata sanarwa da ma'aikatar kudi ta kasar ta fitar a jiya Laraba ta bayyana cewa, gwamnati za ta inganta shirin ta hanyar gudanar da wasu ayyukan gwaji zagaye na hudu.

Gwamnatin tsakiyar kasar dai na daukar shirin hadin gwiwa na PPP a matsayin wata hanya ta daukar nauyin wasu ayyukan more rayuwa, biyo bayan damuwar da ake nunawa dangane da tarin bashin da ake bin kananan hukumomi.

Bayanai na nuna cewa, tattalin arzikin kasar Sin dai na kara canjawa zuwa wanda ke dogara da kayayyakin da ake amfani da su da kuma bangaren samar da hidima, yayin da Sinawa ke kokarin yin rayuwa mai inganci.

A jawabin da ya gabatar yayin taron dandalin Davos na lokacin zafi da ya gudana a watan Yunin da ya gabata a birnin Tianjin dake nan kasar Sin, firaminista Li Keqiang na kasar Sin ya bayyana yadda bangarorin yawon shakatawa, da al'adu da harkokin wasanni, da lafiya ke bunkasa cikin hanzari a kasar ta Sin.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China