in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Al'ummar kasar Afrika ta kudu sun gudanar da bikin ranar samun 'yanci, suna masu kira da yi wa tsarin tattalin arziki garambawul
2017-04-28 09:42:31 cri
Al'ummar kasar Afrika ta Kudu sun gudanar da bikin ranar samun yancin kai a jiya Alhamis, inda suka yi ta kiraye-kirayen yi wa tsarin tattalin arzikin kasar gaggarumin sauyi tun daga tushe, da nufin samarwa bakeken fata 'yanci a fannin tattalin arziki.

An yi wa bikin na jiya da aka sadaukar ga Oliver Tambo, wanda ya taka rawar gani wajen faffutukar yaki da wariyar launin fata, taken 'shekarar Oliver Reginald Tambo, zurfafa tsarin demokradiyya a tare da gina al'ummu cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya'

An gudanar da gangami a sassa daban-daban na kasar domin bikin cika shekaru 23 da kawo karshen wariyar launin fata.

Duk da cewa kasar Afrika ta Kudu ta gina tsarin Demokradiyya a kan tafarkin kare 'yancin dan adam da kundin tsarin mulki, galibin bakaken fata ba su da karfi ta fuskar tattalin arziki, haka zalika, ba su gamsu da nasararorin da tattalin arzikin ya samu ba.

Shugaban kasar Jacob Zuma, ya halarci taron gangami da aka yi a wani yankin dake kusa da birnin Durban, inda a jawabinsa, ya tabbatar da cewa Kasar ta cimma samun 'yanci ta fuskar siyasa amma har yanzu da sauran rina a kaba ta fuskar 'yancin tattalin arziki.

Jacob Zuma ya jadadda cewa, yi wa tsarin tattalin arzikin gagarumin sauyi na nufin tabbatar da sauyi ta fusakar tsari da manufofi da ikon mallaka tare da kula da harkokin tattalin arzikin domin amfanin dukkanin al'ummar kasar, musammam masu karamin karfi da kuma wadanda suka fi rinjaye da suka kasasnce bakaken fata da mata. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China