Wannan ne ziyarrar Zuma ta farko tun sake hayewa karagar mulkin kasar a zagaye na biyu.
A cewar Madam Hua, lokacin ziyarar, Jacob Zuma zai gana da shugaban kasar Sin Xi Jinping da Firaministan kasar Li Keqiang da shugaban majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Zhang Dejiang.
A cikin batutuwan da shugabannin zasu tattauna akwai batun zurfafa dangantakar dake tsakanin sassan biyu da sauran batutuwan da suke janwo hankalan bangarorin biyu.