in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban bankin duniya zai yi iyakacin kokari don inganta hadin gwiwa da bankin AIIB
2015-04-08 11:14:16 cri
A ranar 7 ga wata, a birnin Washington na Amurka, shugaban bankin duniya Kim Jim-Yong ya bayyana fara'a da yakini don ganin bankin saka jari na Asiya wato AIIB da Sin ta yi tayin kafawa, inda ya bayyana cewa, zai yi iyakacin kokari don inganta hadin gwiwa da bankin, don rage talauci a duniya.

A wannan rana, yayin da mista Kim ke jawabi a cibiyar nazarin manyan tsare-tsare da muhimman batutuwan duniya ta kasar Amurka, ya bayyana cewa, bankin AIIB zai zama wani babban abokin hadin gwiwa ga bankin duniya wajen cimma burin rage talauci a duniya.

Ya ce, idan bankin AIIB da bankin raya kasashen BRICS da sauran hukumomin hada-hadar kudi na duniya suka kafa wani kawance a tsakaninsu, sun yi hada gwiwa don tinkarar kalubalen da duniya ke fuskanta, duk kasashen duniya za su samu moriya daga cikinsu, yana fatan wadannan sabbin hukumomi za su yi hadin gwiwa da bankin duniya don sa kaimi ga raya tattalin arziki, da rage talauci a duniya. Yanzu, akwai mutane kimanin biliyan guda da ke rayuwa da kudi kasa da dalar Amurka 1.25 a ko wace rana, kuma suna cikin kangin talauci.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China