in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sama da 'yan kasashen waje dubu 900 ne ke aiki a Sin a 2016
2017-04-17 10:14:30 cri

Wani jami'in kasar Sin ya bayyana cewa, sama da 'yan kasashen waje 900,000 ne suke yin aiki a cikin kasar Sin zuwa shekarar 2016, inda ya bayyana lamarin da cewa, suna taka muhimmiyar rawa ne a kasar ta Sin.

Zhang Jianguo, shugaban hukumar kula da kwararru 'yan kasashen waje ta kasar Sin ya bayyana cewa, kwararrun 'yan kasashen waje muhimmin arziki ne. Ya ce, suna matukar taimakawa kasar Sin wajen samun bunkasuwar tattalin arziki da yanayin ci gaban al'umma, ya furta hakan ne a lokacin taron kasa da kasa game da yin musayar kwararru wanda aka gudanar a birnin Shenzhen dake kudancin kasar Sin.

Domin janyo hankalin karin kwararru daga ketare, kasar Sin ta sassauta hanyoyi samun takardun visa ga kwararru 'yan kasashen waje dake son zuwa kasar Sin don yi ayyuka. Sabon tsarin zai tattara shedar izinin zama da ake bayar su guda biyu a matsayin kwaya daya ga masu yin aiki a saukakawa bakin yadda za su yi aiki a kasar Sin.

Daga shekarar 2001 zuwa 2016, an kara yawan kasashen da kwararru da za su iya zuwa Sin don yin aiki daga 21 zuwa kasashe 73.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China