Majalisar gudanarwar kasar Sin ta sanar a jiya Litinin cewa, za ta samar da guraben ayyukan yi kimanin miliyan 50 a garuruwan kasar nan da shekarar 2020.
Majalisar gudanarwar ta bayyana shirinta na samar da ayyukan yi na shekarun 2016-2020, da cewa muhimmnin batu ne na inganta rayuwar al'umma da kuma habaka ci gaban tattalin arziki.
Kasar Sin ta dukufa matuka wajen samar da ayyukan yi masu yawan gaske, musamman wajen harkokin da suka shafi kasuwanci domin fadada hanyoyin ci gaban tattalin arziki.
Gwamnatin kasar Sin za ta tallafawa dalibai da suka kammala karatunsu, da manoma da ma'aikata, don ba su ayyukan yi, don rage cinkoso a ma'aikatu da kamfanani masu zaman kansu.(Ahmad Fagam)