Hua Chunying na bayyana hakan ne yayin da take amsa tambayar 'yan jarida game da hakan. Ta ce abun mamaki ne a ce wani zai yarda da wannan zargi maras tushe.
Kalaman nata dai na zuwa ne a gabar da wasu jami'an Taiwan ke cewa tun da fari, kasar Sao Tome da Principe ta nemi Taiwan din ta bada wasu kudade masu tarin yawa, kuma rashin aiwatar da hakan ne ya sanya kasar yanke huldar ta da yankin na Taiwan.
Sai dai a daya bangaren uwargida Hua ta ce manufar kasar Sin daya tak a duniya, na da matsayi na musamman a fannin diflomisiyyar kasa da kasa, kaza lika manufa ce ta daukacin al'ummar kasashen.