Kasar Sin da kasar Sao Tome and Principe, sun fitar da hadaddiyar sanarwa a ranar 26 ga wata, inda suka yi shelar maido da dangantakar jakadanci tsakanin kasashen biyu, wadda ta katse kusan shekaru 20.
A wannan rana, ministocin harkokin wajen kasashen biyu, wato Wang Yi na kasar Sin da Urbino Botelho na Sao Tome and Principe, sun yi wata tattaunawa a birnin Beijing, inda suka daddale, suka kuma fitar da hadaddiyar sanarwa, kan dawo da huldar diflomasiyya tsakaninsu.
A cewar sanarwar, gwamnatin kasar Sao Tome and Principe ta amince akwai kasar Sin daya tak a duniya, kuma gwamnatin jamhuriyar jama'ar kasar Sin, halaltacciyar gwamnati ce daya tilo, da ke wakiltar kasar Sin. Sannan, Taiwan wani yanki ne da ba za'a iya balle shi daga kasar Sin ba.
Haka kuma gwamnatin Sao Tome and Principe ta yi alkawarin cewa, ba za ta kulla wata dangantaka da Taiwan ba, haka kuma, ba za ta yi duk wata mu'amala ta fuskar gwamnati da ita ba.
A ganawarsa da kafofin watsa labarai, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya ce, bayan shekaru da dama, gwamnatin kasar Sao Tome and Principe ta yanke shawarar sake amincewa da manufar kasar Sin daya tak a duk duniya, lamarin da ya dace da moriyar al'ummar kasar. A cewar Wang Yi, farfado da dangantakar jakadanci tsakanin kasashen biyu, abu ne mai kyau da zai kawo alfanu ga kasar Sin da kasar Sao Tome and Principe, har ma ga kasashe daban-daban na Afirka.(Murtala Zhang)