in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'an soja daga kasashen Afrika 13 ne suka halarci taron ba da horo a kasar Rwanda
2017-03-26 12:26:23 cri
Kimanin jami'an soja 200 daga kasashen Afrika 13 ne suka halarci taron atisayen soji na hadin gwiwa a kasar Rwanda.

Taron wanda aka fara a ranar Asabar da ta gabata a sansanin sojoji na Galo dake gabashin kasar Rwanda, ya hada da sojojin kasashen Algeriya, Angola, Benin, Burkina Faso, Chadi, Masar, Nijer, Rwanda, Senegal, Afrika ta kudu, Sudan, Tanzaniya da Uganda.

Taron ba da horo na sojin karo na 3 mai taken "Utulivau Afrika III", za a gudanar da shi ne daga ranar 20 zuwa 31 ga wannan wata na Maris.

Ana gudanar da taron ne karkashin shirin horas da dabarun kai daukin gaggawa na Afrika wato ACIRC a takaice.

ACIRC, shiri ne na musamman tsakanin kungiyar tarayyar Afrika AU da kasashen duniya masu aikin sa kai, da nufin taimakawa kungiyar ta AU wajen kai daukin gaggawa da zarar aka samu barkewar tashin hankali a nahiyar Afrika.

A shekarar 2013 ne aka kaddamar da wannan shirin a matsayin shiri na wucin gadi kafin Afrikar ta samu takamammiyar rundunar wanzar da tsaro wacce za ta yi aiki yadda ya kamata. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China