in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron Majalisun NPC da CPPCC da Tasirinsa ga bunkasar duniya
2017-03-09 12:30:36 cri
Taron majalisar wakilan jama'a NPC da na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa CPPCC, wanda aka fi sani da taruka biyu da aka bude ranar 3 ga wata na ci gaba da daukan hankalin duk duniya musamman masana, masharhanta da kuma 'yan jaridu daga sassa daban daban na duniya. Sakamakon yadda tattalin arzikin kasar China ke ci gaba da bunkasa, sa'an nan tasirin sa ke ci gaba da ratsa kowanne loko da sako na fadin duniya a daidai lokacin da sauran kasashen duniya ciki har da masu ci gaba ke fama da mashasharar tattalin arziki.

A kowacce shekara yayin da a ke gudanar da taruka biyu bisa al'ada, mahalarta taron kan yi kokarin gudanar da taza da tsifa ga tsarin tattalin arzikin kasa tare da bibiyar manufofin gwamnati daya bayan daya da nufin kwaskware su duk domin tabbatar da cewa tattalin arziki na tafiya kan gwadabe mai kyau, kuma dangantaka tsakanin kasar Sin da sauran kasashe na kara inganta. A sa'i daya kuma a tabbatar da tsarin zamantakewar al'umma na kara kyautatuwa. Kawo yanzu za a iya cewa, kwalliya ta biya kudin sabulu, dangane da tsare tsare da sauran manufofin gwamnati da taruka biyu ya haifar.

Misali, bayan da kasar Sin ta samu nasarar 'yanta kimanin mutane miliyan 750 daga kangin talauci cikin shekaru 30 kawai, ta kuma aza harsashin ceto sauran mutane miliyan 250 wanda har yanzu suke fama da fatara nan da shekara ta 2020 karkashin shirin raya kasa na shekaru biyar biyar, wanda ya hada da batun kawo karshen matsalar gurbatar iska, da rungumar makamashi mai tsafta ga ababen hawa da masana'antu.

Bayan da sakamakon taruka biyu ya kawo dimbin alheri ga kasar Sin cikin kankanin lokaci, manufofin taron sun kai ga daga darajar kasar Sin zuwa kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a fadin duniya. Sa'an nan, tasiri da kuma irin rawar da kasar Sin ke takawa a fagen raya tattalin arzikin duniya shi ma ya ci gaba da karuwa. Alal misali, ya zuwa shekarar bara ta 2016 yawan jarin da kasar Sin ta zuba a ketare ya kai matsayi na koli, wato ya kai dalar Amurka biliyan 189. Ban da wannan, darajar cinikayya tsakanin kasashen nan dake hadin gwiwa da Sin karkashin shirin nan da kasar ta Sin ta bullo da shi wato Ziri daya hanya daya ya kai na dala biliyan 236.

Kazalika, asusun bayar da lamuni na duniya IMF ya gabatar da wani rahoto a shekarar bara ta 2016 inda ya ke cewa, kasar Sin ta ba da gudunmawa ga bunkasar tattalin arzikin duniya da fiye da kashi 30% cikin dari. Wannan ra'ayi ya zo daidai da na wani masani dan kasar Amurka Stephen Roach wanda ya kara jaddada tasirantuwar tattalin arzikin duniya a kan China. Lamarin dake nuna cewa kayayyakin kasar Sin suna da farin jini a kasuwa. Wannan wata kyakkyawar shaida ce dake haska cewa, taruka biyu sun haifar da sakamako mai kyau ga kasar Sin da ma duniya aki daya, hakan nan zai taimaka wajen kara wa kasar Sin kima da daraja a idon duniya.

Ita ma nahiyar Afirka ba a barta a baya ba wajen cin gajiyar manufofin ba da tallafi ga kasashe masu tasowa, domin a shekarar bara ta 2016 kasar Sin ta kebe dalar Amurka biliyan 60 don tallafa wa nahiyar musamman a fannin samar da ababen more rayuwa wanda Afirkan ke kamfar su.

A hakikanin gaskiya, idan tattalin arzikin kasar Sin ya ci gaba da habaka da kashi 6.5% kamar yadda firaministan kasar Sin Li Keqiang ya labarta cikin rahoton aikin gwamnati, to lalle kasar China za ta ci gaba da taka rawar a zo a gani a fagen raya tattalin arzikin duniya.

Mai sauraron ku a kullum

Nuraddeen Ibrahim Adam

Shugaban kungiyar

Great Wall CRI Listeners' Club

Kanon Dabo, Nigeria

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China