in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Tanzania ya karbi aikin filin jirgin da Sin ta sake ginawa
2017-03-07 10:04:09 cri

Shugaba John Magufuli na kasar Tanzaniya, ya kaddamar da filin jirgin sama na soji da kasar Sin ta yi aikin sake ginawa, a Ngerengere dake yankin Morogoro dake kasar.

Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar, ta rawaito shugaba Magufuli na godewa kasar Sin, bisa taimakon da ta yiwa Tanzania wajen sake ginin filin jiragen saman na soji bayan lalacewar sa.

Shi ma a nasa bangare, babban hafsan dakarun tsaron kasar Tanzaniya Venance Mabeyo, ya ce sai a wannan lokaci ne aka sake ginin filin jirgin, tun bayan gina shi karon farko a shekara ta 1970.

Mabeyo ya ce, an kashe kudi har dalar Amurka miliyan 68.5, tun bayan fara gyaran filin jirgin a cikin watan Yulin shekara ta 2013. Kaza lika gyaran fuskar da aka yiwa filin jirgin, ta kunshi fadada titin tashi da saukar jirage.

Mr. Mabeyo ya ce, yanzu haka wannan filin jirgi na cikin irin sa mafiya nagarta a dukkanin fadin duniya, zai kuma iya daukar manyan jiragen dakon kaya, da na fasinjoji ba tare da wata tangarda ba.

Da yake maida jawabi kan hakan, jakadan kasar Sin a kasar Lu Youqing, ya ce wannan aiki da Sin ta gudanar a Tanzania, na dada shaida irin dankon zumunta dake ci gaba da wanzuwa tsakanin sassan biyu.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China