in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tanzaniya ta yi alkawarin karfafa dangantaka da kasar Sin
2017-01-22 12:51:21 cri

Mataimakin shugaban kasar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan, ya sanar a jiya Asabar cewa, kasarsa za ta ci gaba da daukar matakai don karfafa dangantaka tsakaninta da kasar Sin domin cin moriyar al'ummomin kasashen biyu.

Hassan ya bayyana hakan ne a lokacin bikin murnar sabuwar shekarar Sinawa wanda aka gudanar a dandalin taro na Mnazi Mmoja dake babban birnin kasar Darussalam. Bikin ya samu halartar Sinawa da kuma 'yan kasar Tanzaniyan mazauna babban birnin kasar.

Mataimakin shugaban kasar ya ce, kasar Sin babbar abokiyar huldar Tanzaniya ce tun shekaru masu yawa da suka gabata, ya kara da cewa, dangantakar dake tsaknin kasashen biyu tana kara samun bunkasuwa.

Hassan ya baiwa jakadan Sin a Tanzaniya Lu Youqing tabbaci cewa, gwamnatin shugaban kasar Tanzaniyan John Magufuli za ta yi hulda ta kut da kut da gwamnatin Sin wajen habaka harkokin cinikayya, da ilmi, da kiwon lafiya da kuma musayar al'adu.

Hassan ya ce, kasar Tanzaniya tana da abubuwan koyi masu yawa daga kasar Sin, musamman game hanyoyin bunkasa ci gaban tattalin arziki wanda kasar Sin ta yi matukar fice a fannin.

A nasa bangaren, ambasada Lu, ya yabawa kasar Tanzaniya bisa irin matakan da take dauka na yaki da rashawa.

A ranar 14 ga wannan watan ma, tsohon shugaban kasar Tanzaniya Benjamin Mkapa ya yabawa kasar Sin saboda haramta fataucin hauren giwa da kasar ta yi, kana ya bukaci kasashen duniya da su bi sahun kasar ta Sin game da wannan batu.

Mkapa wanda ya shugabanci kasar Tanzaniya tsakanin shekarun 1995 zuwa 2005, ya ce daukar irin matakin da kasar Sin ta yi na haramta fataucin hauren giwar, zai hana giwaye bacewa daga doron kasa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China