in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara aiki da cibiyar watsa labaran taruka biyu na Sin
2017-02-28 10:14:41 cri
Za a bude taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a ranar 5 ga wata mai zuwa da kuma taron majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar a ranar 3 ga watan, wato muhimman taruka biyu na kasar Sin. A jiya Litinin ne, cibiyar watsa labarai game da tarukan biyu da aka kafa a nan birnin Beijing ta fara aiki.

Jami'in da ke kula da cibiyar ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu, 'yan jarida na gida da na waje sama da 3000 ne suka yi rajistar ba da labaran tarukan biyu, kuma daga cikinsu, yawan 'yan jarida da suka zo daga babban yankin kasar Sin da kuma Hongkong da Macao da Taiwan sun yi daidai da na bara, a yayin da 'yan jarida na kasashen ketare ke ci gaba da karuwa. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China