A gobe Jumma'a ne za a bude taron shekara shekara na bana na majalissar ba da shawara kan harkokin siyasar kasar Sin CPPCC a nan birnin Beijing.
Da yake tabbatar da hakan a Alhamis din nan, kakakin zaman majalissar na wannan karo, Mr. Wang Guoqing, ya ce ana sa ran bude zaman majalissar ne da misalin karfe 3 na rana, zaman da kuma zai samu halartar mambobi sama da 2,000 daga sassan kasar daban daban.
Ana sa ran yayin zaman, za a tattauna game da batutuwa da suka jibanci muhimman harkokin siyasa, da na tattalin arziki da zamantakewar al'umma, wadanda ke da nasaba da shirin ci gaban kasar ta Sin na shekaru biyar biyar.
Majalissar CPPCC dai ita ce mafi girma a kasar Sin wajen bada shawarwari game da hanyoyin ciyar da kasa gaba. Za kuma ta kammala taron ta na wannan karo ne a ranar 13 ga watan Maris din nan.(Saminu Alhassan)