in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu bada tallafi na bankin duniya sun amince da samar da dalar Amurka biliyan saba'in da biyar domin kawar da fatara
2016-12-16 13:41:51 cri
Sama da gwamnatoci masu ba da rance da masu karbar sittin ne suka amince da samar da dala biliyan saba'in da biyar ga kungiyar raya kasashen waje IDA, wanda shiri ne na bankin duniya dake da nufin kawo karshen matsanancin talauci.

Wata sanarwa da bankin duniyan ya fitar yau Alhamis, ta ce kudin zai taimaka wajen gaggauta tallafin da kungiyar ke bayarwa, tare da samar da ayyukan yi da damammakin habaka tattalin arziki ga kasashen duniya dake fama da talauci.

Sanarwar ta ruwaito shugaban bankin Jim Yong Kim, na cewa, shirin wani gagarumin mataki ne na kawo karshen fatara.

Shirin dai, na da nufin kara yawan tallafinsa tsakanin 1 ga watan Yulin 2017 zuwa 30 ga watan Yunin 2020,a fannonin kiwon klafiya da rage talauci da samar da ilimi da ruwan sha da hasken wutar lantarki, ga miliyoyin yara da manya.

Kimanin kasashe 75 masu karancin kudaden shiga ne suka cancanci cin gajiyar wannan shiri.(Fa'iza)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China