in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabunta: Kasar Sin tana bibiyar batun mutuwar Kim Jong Nam
2017-02-16 18:59:17 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya shaidawa taron manema labarai a jiya Laraba cewa, kasar Sin tana bibiyar dukkan rahotannin da kafofin watsa labarai ke watsawa game da mutuwar Kim Jong Nam.

Geng ya ce, mahukuntan kasar Sin suna sane da wannan labari, kuma bisa iya saninsu, lamarin ya faru ne a kasar Malaysia, a saboda haka, mahukuntan kasar ta Malaysia suna gudanar da bincike game da wannan lamari.

Ofishin jakadancin kasar Koriya ta arewa dake Malaysia ya tabbatar da cewa mutumin dan shekaru 46 da haihuwa, wanda ke rike da fasfo da sunan Kim Chol, a hakika shi ne dai Kim Jong Nam.

Tuni kuma wasu kafofin kasar suka rawaito mataimakin firaministan kasar ta Malaysia Ahmad Zahid Hamidi na tabbatar da hakan. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China