in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan sanda a Malaysia sun cafke wata da ake zargin na da alaka da kisan dan uwan shugaban Koriya ta arewa
2017-02-15 19:54:17 cri
Rundunar 'yan sandan kasar Malaysia, ta ce ta samu nasarar kame wata mace, wadda ake zargin tana da alaka da kisan yayan shugaban kasar Koriya ta arewa.

Shugaban rundunar Khalid Abu Bakar, ya bayyana ta wata sanarwa cewa, mace wadda ke dauke da fasfo na kasar Vietnam, ta shiga komar 'yan sanda ne, bayan da aka gane kamanninta daga kyamarorin dake filin jirgin saman birnin Kuala Lumpur. An ce an cafke mace ce ita kadai.

Tuni dai kafofin watsa labaran Koriya ta arewa suka tabbatar da cewa Kim Jong Nam mai shekaru 46 ne aka kashe, a filin jirgin na kasar ta Malaysia a ranar Litinin, kuma yaya ne shi ga shugaban kasar mai ce Kim Jong Un.

Yanzu haka dai gawarsa na can wani babban asibitin kasar ta Malaysia, inda ake ci gaba da gwaje gwaje a kanta. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China