Rahoton ya yi nuni da cewa, koda yake ana samun ingantuwar tattalin arziki a yankin Afirka da ke kudu da hamadar Sahara ta hanyar gina muhimman kayayyakin more rayuwa, duk da haka matsalar rashin ayyukan tana kara tsananta a kasashen dake yankin. Kididdigar kungiyar kwadago ta duniya wato ILO ta nuna cewa, yawan mutanen da suka rasa ayyukan yi a yankin Afirka da ke kudu da hamadar Sahara a shekarar 2017 zai kai kashi 7.2 cikin dari bisa na bara, amma ana hasashen cewa yawansu zai karu zuwa miliyan 29. (Zainab)