in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta goyi bayan kwamitin sulhun MDD game da tsawaita wa'adin tawagar musamman dake yankin yammacin hamadar Sahara
2016-04-30 13:05:25 cri

Kwamitin sulhu na MDD ya zartas da kuduri a jiya Jumma'a cewa, ya tsawaita wa'adin tawaga ta musamman dake yankin yammacin hamadar Sahara zuwa ranar 30 ga watan Afrilu na shekara mai zuwa, kana ya jaddada farfado da ayyukan tawagar a dukkan fannoni.

A wannan rana, zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Liu Jieyi ya yi jawabi bayan kammala taron, inda ya bayyana cewa, kudurin ya bayyana aniyar kwamitin sulhu MDD wajen daidaita batun yammacin hamadar Sahara ta hanyar siyasa.

Kasar Sin ta goyi bayan wannan kuduri, tana fatan tawagar za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da kudurin kwamitin sulhu na MDD da kuma shimfida zaman lafiya a yankin yammacin hamadar Sahara.

Bugu da kari, Liu Jieyi ya bayyana cewa, kasar Sin ta nace ga matsayinta kan batun yammacin hamadar Sahara, kuma zata cigaba da nuna goyon baya ga MDD wajen daidaita batun ta hanyar siyasa, tana fatan bangarori biyu da batun ya shafa za su nemi dabarar daidaita batun ta hanyar yin shawarwari cikin adalci bisa kudurin kwamitin sulhu na MDD.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China