in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gabanin zaben Shugaban kasa, Somalia ta haramta zirga-zirgar jiragen sama, a wani bangare na kara tsananta matakan tsaro
2017-02-08 09:36:11 cri

A jiya Talata ne gwamnatin kasar Somalia ta kara tsananta matakan tsaro, inda ta sanar da haramcin tashi da saukar jiragen sama a filin jirgin saman Mogadishu babban birnin kasar, gabanin zaben Shugaban kasa da za a yi yau Laraba.

Ministan sufurin kasar, Ali Ahmed Jama ne ya sanar da batun dakatar da zirga-zirgar jiragen ga kamfanonin shirya tafiye-tafiye.

Sai dai Ministan ya ce, matakin ba zai shafi sauran filayen jiragen saman kasar ba, tun da zaben zai gudana ne a babban birnin kasar kadai.

Har ila yau, za a rufe dukkan manyan titunan Mogadishu na tsawon kwanaki biyu, har sai an kammala zaben.

Magajin garin Mogadishu Yusuf Jimale ne ya sanya haramci zirga-zirga a kan titunan Mogadishu da nufin tabbatar da tsaro yayin zaben. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China