in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakatare Janar na MDD ya taya Farmajo murnar lashe zaben shugaban kasar Somalia
2017-02-10 13:42:19 cri
Sakatare Janar na MDD, Antonio Guterres ya taya Mohammad Abdullahi Farmajo murnar lashe zaben shugaban kasar Somalia, yana mai bayyana fatan zababben shugaban kasar zai gaggauta kafa gwamnatin da za ta kunshi dukkan bangarori.

Wata Sanarwar da kakakin Sakatare Janar din ya fitar a jiya Alhamis, ta ruwaito Antonio Guterres na kira ga sabuwar gwamnatin da gwamnatocin jihohi su yi aiki tare, wajen gaggauta magance muhimman batutuwan kasar, ciki har da kammala samar da kundin tsarin mulki da kafa managartan matakan tsaron kasar. ( Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China