in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan wadanda suke aiki a kamfanoni masu zaman kansu na kasar Sin ya ninka sau 10 cikin shekaru 25 da suka gabata
2015-10-26 19:40:46 cri
A yau Litinin ne kungiyar ma'aikatan kamfanoni masu zaman kansu ta kasar Sin ta fitar da wani rahoto game da dangantaka tsakanin tattalin arziki mai zaman kansa da batun samar da guraban aikin yi a kasar Sin, inda ta bayyana cewa, tattalin arziki mai zaman kansa wani muhimmin sashen samar da guraban aikin yi ne a nan kasar Sin.

A shekarar 1990, yawan mutanen da suke aiki a kamfanoni masu zaman kansu ya kai miliyan 22.63, amma ya zuwa shekarar ta 2014, wannan adadi ya kai miliyan 250, wato ya ninka sau 10. Yanzu, wasu daga cikin kamfanoni masu zaman kansu ba sa iya daukar ma'aikata kamar yadda suke so.

A cikin wannan rahoto, an ba da shawara cewa, ya kamata a sassauta sharudan daukar ma'aikata, da kyautata yanayin aiki, da kuma kokarin kawar da bambancin dake akwai a tsakanin sana'o'i da kuma yankuna daban daban.

Sannan ya kamata a kara goyon bayan kamfanoni masu zaman kansu wadanda suke samar da dimbin guraban aikin yi, da bullo da karin manufofin da za su kara taimakawa kokarin da ake na samar da guraban aikin yi, kana a tallafa wa dalibai wadanda suka gama karatu daga jami'a, kuma suke kokarin kafa da raya kamfanoni da kansu. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China