in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rwanda tana haramta sanya niqab ga matan musulmai
2016-07-08 10:47:12 cri

Kasar Rwanda ta sanar da haramta sanya niqab ga matan musulmi, in ji babban jagoran musulmin kasar, Salim Hitimana a ranar Laraba.

Da yake magana a yayin bikin karamar Sallah, wato Aid el-Fitr, a filin wasannin motsa jiki na shiyyar Kigali, mista Hitimana ya bayyana cewa, an dauki wannan mataki ne bisa dalilai na tsaro.

Ya jaddada cewa, 'yan ta'adda suna amfani da niqab domin kawo illa ga tsaro, ba ma a kasar Rwanda ba, har ma a duk fadin duniya.

Alkur'ani mai tsarki ya bukaci mata da su rika rufe wasu bangarorin jikinsu, amma ba fuskokinsu ko hannayensu ba, in ji shugaban addinin. Idan wasu musulmai na fadin cewa, haramcin na sabawa 'yancin yin addini, Sheikh Sindayigaya, kakakin al'ummar musulmi, ya bayyana cewa, wannan mataki na samun goyon baya sosai.

Haka kuma ya bayyana cewa, wasu 'yan mata biyu mabiya addinin musulnci 'yan kasar Rwanda dake sanye da niqab, an cafke su baya bayan nan a filin jiragen saman kasa da kasa na Kigali, kafin su shiga cikin jirgin sama.

A cewar Sindayigaya, 'yan matan biyu suna shirin shiga kungiyar IS. Kimanin kashi 4,6 cikin 100 na al'ummar kasar Rwanda suke bin addinin musulunci. Amma ba a san adadin yawan masu sanya niqab ba. Haka kuma mista Hitimana ya yi kashedi ga al'ummar musulmin Rwanda game da kaifin kishin addini. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China