Mai magana da yawun sakatare-janar na MDD Stephane Dujarric, ya bayyanawa kafofin watsa labarai cewa, Kanada kasa ce dake da hakurin zama tare da al'ummu masu al'adu, da kabilu gami da addinai daban-daban, don haka ya yi imanin cewa, kasar gami da daukacin al'ummarta, za su ci gaba da zama tsintsiya madaurinki daya. Za kuma su nuna matukar adawa da duk wani yunkuri na kawo rikici tsakanin addinai daban-daban.
Rahotanni dai sun bayyana cewa, harin bindigar da aka kai kan wani masallaci dake birnin Quebec da daren ranar Lahadi, ya hallaka mutane 6.
Wasu ganau sun bayyana cewa, 'yan bindiga uku ne suka yi harbin kan mai uwa da wabi a masallacin, lokacin da wasu mutane sama da 40 ke masallacin.
Yanzu haka dai 'yan sanda sun rigaya sun kama wani da ake zargin sa da kai harin. (Murtala Zhang)