in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi tattaunawar shekara-shekara karo na farko tsakanin ministocin harkokin wajen kasashen Sin da Canada
2016-06-02 16:06:58 cri
A jiya Laraba ne a Ottawa, babban birnin kasar Canada, aka yi tattaunawar shekara-shekara tsakanin ministocin harkokin wajen kasashen Sin da Canada karo na farko.

A jawabinsa, ministan harkokin wajen Sin Wang Yi ya bayyana cewa, kasarsa na fatan yin mu'amala tare da kasar Canada, tare da zurfafa hadin kai kan harkokin MDD, da taimakawa MDD wajen ba da jagoranci a fannin kiyaye zaman lafgiya da tsaron duniya, tare kuma da karfafa hadin kai bisa tsarin kungiyar G20, domin inganta dauwamammen ci gaban tattalin arzikin duniya yadda ya kamata.

A nasa bangaren ministan harkokin wajen kasar Canada Stphane Dion ya bayyana cewa, kasarsa na mayar da hankali sosai kan hada kai a tsakaninta da Sin, tana kuma fatan karfafa hadin kai a tsakaninsu a fannonin cinikayya, makamashi, aikin gona, kirkire-kirkire, cudanyar al'adu da dai sauransu, ba ya ga kara hadin kai a harkokin kasa da kasa, da kuma ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu gaba.

Shi ma firaministan kasar Canada Justin Trudeau ya gana da Wang Yi a wannan rana a birnin Ottawa. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China