in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'ar Ngouabi ta Jamhuriyar Kongo ta kunshi abubuwan kasar Sin da dama
2017-01-26 14:33:40 cri


Bayan kulla huldar jakadanci tsakanin kasar Sin da Jamhuriyar Kongo a shekarar 1962, ya zuwa yanzu, mu'amala tsakanin kasashen biyu na bunkasa cikin gaggawa a 'yan shekarun nan, musamman a fannin harkokin ilimi

A watan Maris din shekara ta 2013, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyarar aiki Kongo, inda ya halarci bikin kaddamar da dakin karatu na jami'ar Ngouabi da kasar Sin ta taimaka wajen ginawa.

A halin yanzu, ana kara samun abubuwa da suka danganci kasar Sin a wannan shahararriyar jami'a wato jami'ar Ngouabi dake Jamhuriyar Kongo.

An lakabawa Jami'ar Ngouabi sunan tsohon shugaban Jamhuriyar Kongo wato Marien Ngouabi. Kuma ta kasance jami'a daya tilo mallakar gwamnatin kasar.

A ranar 15 ga watan Yunin shekara ta 2012, an kaddamar da kwalejin Confucius na koyar da harshen Sinanci cikin jami'ar. Kuma wannan kwaleji an samar da shi ne, bisa hadin-gwiwar jami'ar Jinan ta kasar Sin da ita kanta jami'ar ta Ngouabi.

Yanzu haka, ana iya ganin abubuwa na kasar Sin da dama a cikin kwalejin Confucius dake dakin karatu na jami'ar Ngouabi, inda dalibai da dama ke koyon harshen Sinanci.

Shugabar kwalejin Confucius malama Li Na ta bayyana cewa, duba da dangantakar siyasa da tattalin arziki da harkar ilimi dake tsakanin kasashen Sin da Jamhuriyar Kongo a 'yan shekarun nan, akwai matasa da dama dake sha'awar koyon harshen Sinanci, baya ga samun karin makarantun sakandare da suke koyar da harshen.

Domin warware matsalar karancin malaman koyar da Sinanci, kwalejin Confucius ta jami'ar Ngouabi, ta gayyaci kwararrun malamai daga jami'ar Jinan, wadanda suka koyar da malaman Kongon, inda daga bisani aka tura malaman na Kongo zuwa makarantun sakandare domin koyar da harshen Sinanci.

Daga watan Satumbar shekarar 2016 ne aka kaddamar da darussan koyar da Sinanci a dukkanin makarantun sakandare 15 na birnin Brazzaville dake kasar ta Kongo.

Malama Li Na ta kara da cewa, kwalejin Confucius ta jami'ar Ngouabi ta dauki matakai da dama na shawo kan matsalolin da suka shafi koyon Sinanci a kwalejin, kuma ta shirya ayyuka da dama na koyar da harshen. Li ta ce:

"A halin yanzu muna iya taimakawa gami da halartar darussan koyar da harshen Sinanci a cikin makarantu daban-daban na Kongo, inda muke gudanar da harkoki da dama, ciki har da horas da malamai, da sa ido kan darussa, da shirya jarrabawar neman shiga jami'a da sauransu."

Kibouka Sonia, daliba ce dake karatun ilimin lissafi a jami'ar Ngouabi, wadda ke da suna na Sinanci mai dadin-ji wato Huang Xinmeng.

Sonia ta fara karatun Sinanci ne a watan Satumbar shekarar 2015, kuma har ta yi nasarar lashe gasar Sinanci da aka gudanar a Jamhuriyar Kongo a watan Mayun shekara ta 2016, lamarin da ya ba ta damar zuwa kasar Sin a watan Yulin shekara ta 2016 domin halartar wata gasa kan harshen Sinanci.

Yanzu, Sonia ta zama malamar koyar da harshen Sinanci a makarantar sakandare ta Brazzaville, inda ta bayyana cewa:

"Dakin karatun nan na da matukar muhimmanci, domin yana ba dalibai da dama zarafin karanta littattafai, musamman ma littattafan Sinanci. A ganina, kwalejin Confucius na da amfani sosai, la'akari da yadda yake kara dankon zumunci tsakanin kasata da kasar Sin, baya ga bada damar koyon Sinanci, domin akwai malamai na kasar Sin da na Kongo. Bugu da kari, dalibai za su samu damar halartar jarrabawar harshen Sinanci mai suna HSK. Kuma Idan sun ci jarrabawar, za su samu damar ziyartar kasar Sin, da ci gaba da koyon harshen na Sinanci."

A ranar 21 ga watan Nuwambar shekarar 2016 ne, gwamnatin kasar Sin ta mikawa jami'ar Ngouabi wasu sabbin gine-ginen da ta bada gudunmuwar ginawa a cikin makarantar, ciki har da wani ginin ofisoshin shugabannin jami'ar, da wata cibiyar yin rajistar dalibai, da wasu hanyoyi da wuraren ajiye motoci.

Shugaban kungiyar kula da fasahohin gine-gine a jami'ar Ngouabi na kamfanin gine-gine na Beijing dake kasar Sin Mista Zhi Yuxin, ya bayyana cewa, an yi aikin gine-ginen bisa fasahohin zamani gami da tsarin ingancin gine-gine na kasar Sin.

Mista Zhi ya ce:

"Mun yi amfani da fasahohin kasar Sin wajen yin wadannan gine-gine, haka kuma Sin ce ta tsara fasalinsu. Sannan dukkanin kayayyakin gine-ginen daga kasar Sin aka kawo su.."

Har ila yau, Kibouka Sonia ta bayyana ra'ayinta game da abubuwan kasar Sin da ake kara samu a jami'ar Ngouabi, inda ta ce:

"A ganina wadannan abubuwa sun yi ma'ana, domin akwai dadadden zumunci tsakanin al'ummar Sin da Jamhuriyar Kongo. Kasar Sin na taimakawa Kongo wajen samun ci gaba, kuma na ji dadi, ina mai farin ciki da hakan."(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China