in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya na shirin sanya harshen Sinanci cikin manhajan makarantun kasar
2014-05-03 16:37:02 cri
Cibiyar tsara manhajan makarantun kasar Kenya KICD ta kaddamar da shirin tsara darussan makarantun firamare da na midil a kwanan baya, inda aka shirya sanya harshen Sinanci cikin darussan makarantun, abin da ya bayyana cewa, Sinanci zai zama daya daga cikin darussan da za a rika koyar wa makarantar. Masu sauraro, ga cikakken bayani dangane da wannan batu da abokiyar aikinmu Amina za ta karanto muku.

Ya zuwa yanzu, ana koyar da harshen Sinanci a wasu jami'o'in kasar Kenya ciki hadda jami'ar Nairobi, jami'ar Kenyatta da ta Egerton da kuma makarantar Upper Hilll. Ko da yake, a halin yanzu dalibai kalilan ne suka koyi Sinanci, amma wannan adadi yana samun karuwa a shekarun nan. An ba da labari cewa, yawan mutane da suka yi rajistar koyon Sinanci ya kai fiye da dubu biyar, wannan adadi kuma bai kunshi yawan 'yan kasar Kenya wadanda suka koyi Sinanci ta hanyar sauraron rediyo da wadanda suka koya da kansu ba.

"Muhimmin dalilin da ya sa cibiyar ke shirin shigar da Sinanci cikin darussan makarantun firamare da na midil shi ne yawan karuwar mutanen da suka nuna sha'awa sosai wajen koyon Sinanci."

Wata jami'ar cibiyar KICD Madam Lydia Nzomo bayan da ta daddale yarjejeniyar tsara manhajar makarantar da jami'ar Kenyatta, ta bayyana cewa,

"Muna fatan baiwa diliban wata dama mai kyau wajen koyon wani harshe na daban. Saboda haka, shigar da harshen Sinanci da sauran harsuna cikin darussan makarantar na da muhimmanci sosai. Ko da yake, akwai wuya wajen tafiyar da wannan aiki, muna da imanin kammala shi cikin nasara."

Game da kalubalolin da za a fuskanta wajen kaddamar da wannan aiki, ciki hadda karancin malamai a wannan fanni, Madam Lydia ta ce, akwai matsalar rashin isasun malaman da za su koyar da Sinanci a Kenya. Saboda haka, Kenya za ta yi hayar malamai Sinawa masu takardar digiri na koyar da Sinanci da 'yan Kenya da suka gama karatu a harshen Sinanci. A cikin shekarar bara, dalibai goma ne suka gama karatunsu daga jami'ar Nairobi kan Sinanci, kimanin rabinsu suka ci gaba da neman karin ilmi a kasar Sin, kuma akwai wasu dalibai 'yan kasar Kenya da suka sami digiri na farko ko digiri na biyu a kasar Sin a wannan fanni.

Wani dalibi wanda ya koyi Sinanci a jami'ar Kenyatta ya bayyana muhimmancin koyon Sinanci,inda yake cewa

"A ganina, koyon Sinanci na da amfani wajen namen aikin yi nan gaba. A halin yanzu, kasashe da dama na gudanar da harkar ciniki da kasar Sin ciki hadda Kenya, hakan ya sa, koyon Sinanci ya zama wani abu mai muhimmanci saboda ganin yadda tattalin arzikin kasar Sin yake samun bunkasuwa cikin sauri."

Ya zuwa yanzu, Sin ta zama kasar da ta fi zuba jari a kasar Kenya, kuma ita ce ta biyu wajen yin ciniki da Kenya. A bangaren nahiyar Afrika, yawan kudin cinikayya da aka samu a tsakanin Sin da Afrika a shekarar 2013 ya kai dala biliyan 210.2 wanda ya kai wani sabon matsayi.

Wasu iyayen dalibai da suka sami labarin cewa za a bude kwass din Sinanci, suna farin ciki sosai. Madam Amina na da yara hudu, dukkansu suna makarantar firamare a birnin Mombasa, ta ce

"Samar da kos din Sinanci abu ne mai kyau a gare mu. Na farko, ban da Turanci da Kiswahili da yaranmu suke koya, suna iya koyon Sinanci, abin da zai baiwa yaronmu damar neman aikin yi a kasar Sin. A matsayina na mahaifiyar su, ina farin ciki sosai ganin cewa, idan suka koyi Sinanci,ni ma suna iya koyar da ni."

Daliban wadanda za su ci gajiyar wannan shiri, sun nuna himma da gwazo sosai kan koyon Sinanci, wani daga cikinsu ya ce

"Ko da yake, koyon Sinanci na da wuya, amma malamansu na da kwarewa sosai, zan yi kokari na kara samun wasu horaswa a gida." (Amina)


Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China