in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Netanyahu ya yi tir da kalaman John Kerry
2016-12-29 09:25:03 cri

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya yi watsi da kalaman da sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya furta, game da manufar Amurka a Gabas taTtsakiya, yana mai cewa, Kerry ya mai da Isra'ilar saniyar ware.

Cikin wani jawabi da ya gabatar ta kafar talabijin a jiya Laraba, Netanyahu ya ce, nacewar da Kerry ya yi ga batun gina matsugunar Yahudawa tamkar barin jaki ne ana dukan taiki.

Ya ce, abun takaici ne yadda babban jami'in diflomasiyya na kasa irin Amurka, zai tsaya yana bata lokacin sa game da wannan batu maras ma'ana.

Daga nan sai ya bayyana fatan gwamnatin sa tare da gwamnatin Amurka mai jiran gado, za su cimma nasarar soke kudurin da aka zartas a zauren MDD, wanda ya la'anci mamayar da Yahudawa ke yiwa yankunan Falasdinawa.

Kafin hakan dai cikin wani jawabi da ya gabatar, Mr. Kerry ya ja kunnen Isra'ila da ta dakatar da fadada gine ginen da take yi a yankunan Yahudawa, yana mai cewa, hakan na barazana ga burin da ake da shi, na kafa kasar Falasdinu tare da kasar Yahudawa bai daya.

Sai dai jim kadan da hakan, shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump, ya aike da sako ta shafin sa na Twitter, yana mai nuna goyon bayan sa ga Israel. Mr. Trump, ya ce yana fatan Yahudun za su juri har ya zuwa lokacin da zai kama aiki a ranar 1 ga watan Janairun dake tafe, domin sauya al'amura.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China