Ned Price, mai magana da yawun kwamitin tsaro karkashin fadar White House, ya bayyana a jiya Jumma'a cewa, kasar Amurka ta tsaya kan manufar ne bisa yarjejeniyar da ta kulla tare da kasar Sin. Haka zalika, samun kwanciyar hankali a zirin Taiwan ya dace da moriyar kasar Amurka, in ji jami'in.(Bello Wang)