in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An binne tokar gawar Fidel Castro Ruz a birnin Santigo na kasar Cuba
2016-12-05 10:53:15 cri
A jiya Lahadi 4 ga wata, an binne tokar gawar Fidel Castro Ruz, shugaban juyin juya halin kasar Cuba a makabartar Santa Ifigenia dake birnin Santigo, tare da kawo karshen zaman makoki na kwanaki 9 na nuna juyayin rasuwarsa.

Bayan isowar motar dake dauke da tokar gawar Fidel Castro Ruz a makabartar Santa Ifigenia, iyalai da abokan Castro sun gudanar da wani kebabben bikin jana'iza.

A kan hanyar zuwa makabartar Santa Ifigenia, miliyoyin 'yan kasar ne suka fito kan hanyar domin yin ban kwana da Castro. Wakilinmu ya gano cewa, ban da jama'ar Cuba, mutane daga Venezuela, da Ecuador, da Rasha da sauransu su ma sun zo domin nuna masa jana'iza.

A daren ranar 25 ga watan Nuwamban bana, Fidel Castro Ruz ya riga mu gidan gaskiya, yana da shekaru 90 a duniya.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China