in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi taron kafofin watsa labarai na Sin da kasashen gabashin Afirka a Kenya
2016-12-02 10:17:56 cri

Jiya Alhamis an gudanar da taron tattaunawa kan aikin kafofin watsa labarai na kasar Sin da kasashen Afirka dake yankin gabashin nahiyar a Nairobin kasar Kenya. Mahalartan taron sun yi musanyar ra'ayoyi kan batutuwan dake shafar kara habaka dandalin yin hadin gwiwa, da kara zurfafa cudanyar kwararru, da kara karfafa cudanya a fannin kafofin watsa labarai na zamani, da kara taka muhimmiyar rawa a cikin harkokin duniya da dai sauransu, haka kuma sun cimma matsaya daya.

An kira taron ne a daidai lokacin da aka cika shekara daya da kammala taron kolin Johnnesburg na dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka, dalilin da ya sa haka shi ne domin tabbatar da sakamakon da aka samu a dandalin, tare kuma da kara karfafa hadin gwiwa mai yakini dake tsakanin kafofin watsa labarai na sassan biyu wato Sin da kasashen dake yankin gabashin Afirka.

Yayin taron, mataimakin shugaban ma'aikatar yada manufar kasar Sin Sun Zhijun ya bayyana cewa, kamata ya yi kafofin watsa labarai na sassan biyu su yi kokari tare domin ciyar da hadin gwiwa dake tsakaninsu gaba yadda ya kamata.

Wakilai mahalartan taron suna ganin cewa, hadin gwiwa dake tsakanin kafofin watsa labarai na Sin da Afirka ya riga ya samu babban ci gaba, suna fatan za a kara karfafawa zuciyar masu aikin watsa labarai, musamman ma matasa su kai wa juna ziyara domin kara kyautata aikinsu. A sa'i daya kuma, ana fatan sassan biyu su yi kokari tare domin biyan sabbin bukatun aikinsu a sabon yanayin da ake ciki, ta yadda za a daga matsayin aikinsu.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China