in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi ganawa a tsakanin shugabannin kasashen yammacin duniya 6
2016-11-19 13:21:12 cri
A jiya Juma'a, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta gana da shugaban kasar Amurka Barack Obama, da shugabannin kasashen Birtaniya, Faransa, Spaniya da Italiya a birnin Berlin na tarayyar Jamus. Bayan ganawar tasu shugaba Obama ya bayar da sanarwa cewa, kasashe mahalarta taron sun nuna goyon bayan azawa Rasha takunkumi.

Bayan da Obama ya gana da firaministar kasar Birtaniya Theresa Mary May, da shugaban kasar Faransa François Hollande, da firaministan kasar Spaniya Mariano Rajoy da firaministan kasar Italiya Matteo Renzi da shugabar gwamnatin Jamus Merkel ya bayar da sanarwa cewa, dukkan shugabannin kasashen 6 suna ganin cewa, idan kasar Rasha ba ta aiwatar da yarjejeniyar Minsk ba, tilas ne a tabbatar da kakabawa Rashar takunkumi, da nuna goyon baya ga tsawaita wa'adin saka takunkumin.

Sanarwar ta kara da cewa, ana nuna damuwa game da rashin tsagaita bude wuta a dogon lokaci, tilas ne a tabbatar da yin tsari game da rikicin kasar Ukraine, da kuma gudanar da zabe cikin adalci a jihohin Donetsk da Luhansk da sauran jihohin dake gabashin kasar Ukraine.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China