in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha na shirya wata ganawa tsakanin Abbas da Netanyahou
2016-10-31 11:02:11 cri
Wani babban jami'in kungiyar kwato 'yan Palesdinu (OLP) ya bayyana a ranar Lahadi cewa kasar Rasha ta fara shirye shirye domin wata ganawa a Moscow tsakanin shugaban hukumar Palesdinu Mahmoud Abbas da faraministan Isra'ila Benyamin Netanyahou.

Ahmad Majdalani, mamban kwamitin zartaswa na OLP, ya jadadda cewa fadar Kremlin ba ta aike da takardar gayyata ba, amma ta bukaci hukumar Falasdinawa da ta shirya kan wannan dandalin na bangarori uku.

An sami labarin daga Rasha cewa tana maida hankali sosai kan dukkan shirye shiryen ganawa tare da Netanyahou, tare da kawar da dukkan shingayen dake kan hanya kafin a aike da takardun gayyata a hukumance, in ji jami'in.

Jami'in ya kara da cewa faraministan Rasha Dmitri Medvedev, zai isa Isra'ila da gabar yamma ta kogin Jordan a ranar 10 ga watan Nuwamba, domin tattaunawa kan wannan batu.

Ahmad Majdalani ya bayyana cewa bangaren Palesdinu a shirye yake ga duk wata ganawa tare da bangaren Isra'ila idan har wannan ganawa zata gudana cikin gajeren lokacin da aka tsaida kuma zata taimaka wajen samar da sakamako mai kyau. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China