in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Guy Ryder ya zarce a kan mukamin babban direktan hukumar ILO
2016-11-08 10:50:08 cri
Hukumar kwadago ta duniya wato ILO mai hedkwata a birnin Geneva ta bayar da sanarwa a jiya Litinin cewa, majalisar zartarwar hukumar ta sake zabar Guy Ryder a karo na biyu a matsayin babban direktan hukumar. Yanzu wa'adinsa zai kare ne a watan Satumba na shekarar 2017, don haka sabon wa'adinsa zai fara daga ranar 1 ga watan Oktoba na shekarar 2017, wato karin shekaru 5 masu zuwa.

A jawabinsa bayan sake zabensa, Ryder ya bayyana cewa, za a ci gaba da yiwa dokokin kwadago kwaskwarima. Haka kuma zai ci gaba da kokarin samar da daidaito a tsakanin al'umma kamar yadda dokokin gwamnatocin kasashe da kamfanoni da na kwadago suka tanada. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China