Babban jami'in zartaswa na kungiyar ILO Guy Ryder ya bayyana a yayin bikin bude taron cewa, kasashen duniya sun shiga wani yanayi na kirkiro sabbin fasahohi, da samar da kayayyaki, da raya zaman rayuwa tare. Ya jaddada cewa, idan aka ci gaba da nuna halin ko'in kula game da rashin daidaito a duniya, babu shakka lamarin zai shafi kowa. Ryder ya yi kira ga kwamitin wakilan ma'aikata da shugabannin kamfanoni da na gwamnati da su yi kokarin kiyaye mutuncin aiki, don warware rikici ta hanyar samar da guraben aikin yi da sauransu.(Bako)